An soma taron sake gina Ukraine | Labarai | DW | 04.07.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soma taron sake gina Ukraine

A wannan Litinin aka bude taron sake gina kasar Ukraine a Lugano na kasar Switzerland. Amma masu sharhi na ganin ana son riga malam masallaci a gina kasar da ke tsakiyar yaki.

Wakilai daga kasashen duniya kusan arba'in da wasu kungiyoyi masu zaman kansu ne suka hallara a birnin Lugano na kasar Switzerland da zummar shata matakan da za a bi a sake gina kasar Ukraine da yaki ya daidaita. Ukraine za ta gabatar da bukatunta a gaban taron da zai dukufa wajen gyara kasar.

Manufar taron a bi tsarin da aka yi amfani da shi wajen nasarar sake gina Turai bayan yakin duniya na biyu, amma kafin soma taron da dama suka soma diga ayar tambaya kan manufarta, wasu na ganin ana son riga malam masallaci ganin har yanzu, ba wai an kawo karshen yakin ba kuma Rasha na ci gaba da yi wa Ukraine luguden wuta.