An soke ziyarar da Kofi Annan zai kai Iran a makon gobe | Labarai | DW | 05.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soke ziyarar da Kofi Annan zai kai Iran a makon gobe

Bayan kalaman nuna kyamar Isra´ila da shugaba Mahmud Ahmedi-Nejad na Iran yayi, babban sakataren MDD ya soke ziyarar da ya shirya kaiwa Iran cikin mako mai zuwa. Wata sanarwa da MDD ta bayar a birnin New York ta ce an cimma wannan daidaito ne tsakanin mahukuntan birnin Teheran da mista Annan, cewar bai dace ba babban sakataren na MDD ya kai ziyarar a wannan lokaci. A cikin makon gobe ne dai Annan zai wani rangadin kasashen yankin GTT. A cikin makon jiya kwamitin sulhu na MDD yayi tir da kalaman da shugaba Ahmedi-Nejad yayi na a shafe Isra´ila daga taswirar duniya.