An soke zaben shugaban kasa na Austria | Labarai | DW | 01.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soke zaben shugaban kasa na Austria

Babbar kotun tsarin mulki kasar Austria ta soke sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na biyu wanda aka gudanar a cikin watan Mayun da ya gabata.

Zaben wanda jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta FPÖ ta Norbert Hofer ta sha kaye a gaban jam'iyyar masu rajin kare muhali ta Alexander Van der Bellen,na zuwa ne mako daya bayan da Birtaniya ta ba da sanarwar ficewa daga EU.

Jam'iyyar ta masu ra'ayin rikau ita ce ta shigar da kara kuma kotun ta ce an yi kura-kurai a zaben na shugaban kasa a cikin sama da kuriu dubu 700 wadanda aka ka'da ta hanyar aikewa da sako.Yazuwa yanzu dai ba a bayyana ranar da za a sake yin wani sabon zabe ba a kasar.