An samu bullar sabon nau’in cutar Polio a Najeriya | BATUTUWA | DW | 24.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

An samu bullar sabon nau’in cutar Polio a Najeriya

Hukumomin lafiya a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da bullar wani sabon nau'in kwayar cutar Polio.

An gano wannan kwayar cutar ce ta hanyar binciken wasu magudanan ruwa a cikin birnin Bauchi, lamarin ya tada hankalin jama’a kasancewa kwayar cutar ta banbanta da wacce aka sani a baya. Zuwa yanzu dai ma’aikatar lafiya ta jihar Bauchi ta fara daukar matakan yakar wannan cuta inda aka debi jinin yara kimanin hamsin a sassa daban-daban na jihar domin tantance hakikanin cutar da kuma shawo kanta kafin ta kai ga wani mataki da dakile ta zai yi wahala. Dr Zuwaira Ibrahim Hassan ita ce kwamishinar lafiya a jihar Bauchi.

“Irin wannan kwayar cutar da aka gano a cikin kwatami an yi shekara bakwai ba a same shi ba. An gano kwayar cutar ce a magudanan ruwa na wasu yankuna uku da suka hada da Dankadai da Makama "B" da kuma Hardo. A yanzu ana ci gaba da gwaji akan kwayar cutar“

Lura da irin yadda kwayar cutar shan inna take nakasa yara, shin ko wannan sabuwar ma tana iya yin illa wa yara makamanciyar wacce ta da din take yi. Pharmacist Adamu Ibrahim Gamawa shine shugaban hukumar lafiya a matakin farko a jihar Bauchi.

“Ba dole ne don kwayar cutar ta shiga jikin yaro ta nakasa shi ba, amma kuma tana iya yiwuwa tun da cutar ta rikide. Wani lokacin ta kan rikide ta zama mai cutarwa.”

Yanzu dai ana iya cewa aiki ya dawo sabo dangane da kokarin da hukumomin lafiya a matakin kasa da jihohi ke yi na dakile yaduwar wannan cuta wacce ta zo a dai-dai lokacin da hukumar lafiya ta duniya ke dab da ayyana Najeriya cikin jerin kasashen da suka yaki cutar ta Polio.

Sauti da bidiyo akan labarin