An sami mutane biyu da Ebola a Najeriya | Labarai | DW | 22.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sami mutane biyu da Ebola a Najeriya

Ma'aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya ta ce mutaneda suka kamu da Ebola ba su hadu kai tsaye da Patrick Sawyer wanda ya shigo Najeriya da cutar kafin ya gamu da ajalinsa ba.

A Najeriya, an sake gano wasu mutane biyu masu dauke da cutar Ebola, a wani abin da ke tayar da hankali. Kuma an gano cewa ba su ma cikin masu kula da lafiyar da suka kula da dan Laberiyan nan da ya shigo Najeriya da cutar.Ministan lafiyan kasar ne Mr Onyebuchi Chukwu ya bayyana hakan lokacin ganawar da ya yi da manema labarai.

Mutanen biyu, suna auren wadanda suka kula da shi mamacin Patrick Sawyer ne lokacin da ya iso Najeriyar a watan da ya gabata, har wasu mutane 11 su ma suka kamu da cutar. Tun farko dai mahukuntan Najeriya sun ce babu wani babban hadari kamuwa da cutar domin tun kafin ya dade cikin bainar jama'a aka killaceshi.

Wadannan mutane da aka gano ya kai adadin wadanda suka kamu da cutar zuwa 14 wato har da Patrick Sawyer. A cikinsu kuma mutane biyar suka rasu, a yayin da wasu biyar kuma suka sami sauki har aka sallamesu daga asibiti. Har yanzu kuma wasu hudun suna jinya a wani wuri inda aka killac su a jihar Legas ta Najeriya inda jirgin da ya dauka Patrick Sawyern ya sauka.

Cutar dai ta fi kamari ne a kasashen Liberiya Gini da Saliyo, inda Liberiya ke kan gaba da yawan mace-mace kusan 600.

Mawallafi: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe