An saki uwargidan Hama daga sabon kamu | Labarai | DW | 05.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki uwargidan Hama daga sabon kamu

Wata kotu a birnin Yamai ta saki Hadiza Hama Amadou uwargidan tsohon shugaban majalisar dokoki Nijar, da kuma Alhaji Moussa Hayatou, tsohon babban darektan banki.

Mutanan biyu na daga cikin wadanda ake tuhuma da matsalar safarar jarirai a Jamhuriyar naijar. An sallemesu ne bayan da suka shafe kwanaki biyu a tsare a ofishin 'yan sanda dake kula da bincike a birnin Yamai, lokacin da suke kokarin barin birnin na Yamai zuwa garuruwansu dake cikin kasar ta Nijar.

Ita Hajia Hadiza Hama Amadou ke tare ne da mahaifiyarta a lokacin da ke zuwa birninTahoua, yayin da shi kuma Moussa Hayyataou, ke bisa hanyarsa ta zuwa garin Kore Mairuwa dake cikin jihar Dosso, don wasu bukatunshi. Duk da cewa babu wata hujjar da zata han su zuwa wannan bulagoro, an dora masu laifin barazanar tayar da tarzoma a bakin get din na 'yan sanda, zargin da daya daga cikin lauyoyin dake kar su, Barista Nasirou Lawali, ya musanta.