An saki masu zanga-zanga a Legas | Labarai | DW | 13.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki masu zanga-zanga a Legas

Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta sallami wasu daga cikin jerin matasa masu zanga-zangar sake bude Lekki gate da ke Lagos a kudancin Najeriya.

An sallami wasu matasan da aka cafke biyo bayan da suka yi kokarin hada gangamin nema wa mutane 12 da suka mutu a yamutsin watan Oktobar bara, adalci.

An dai yi gangamin ne da sunan Allah wadai da cin zalin da 'yan sandan rundunar SARS ke yi a kasar.

'Yan gwagwarmaya ne dai suka yi boren a yau, bayan bude Lekki gate, wato wajen da aka yi zargin sojoji da buda wuta a kan matasan, inda suke cewa ba su ga dalilin sake bude wajen da gwamnati ke samun biliyoyin nairori ba, lamarin da ya kai jami'an 'yan sandan afka masu tare da yin awon gaba da fiye da mutun 30 da suka so yin gangamin.