1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace limanin coci dan Italiya a Niger

Abdullahi Tanko Bala
September 18, 2018

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da sace wani Limamin coci dan kasar Italy da ke aikin mishin a iyakar kasar da Burkina Faso 

https://p.dw.com/p/356Vw
Symbolbild Katholische Kirche
Hoto: Imago

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da sace wani Limamin coci dan kasar Italy da ke aikin mishin a iyakar kasar da Burkina Faso 

Rahotanni sun ce a tsakar daren ranar Talata ce wasu mutane akan babura suka kai farmaki gidan Limamin cocin Pier Luigi Maccalli da ya shafe tsawon lokaci yana aikin addini a yankin Makolandi da ke da tazarar kilo mita 130 a yamma maso kudancin kasar 

Kakakin gwamnatin Niger Malam Zakariya Abdourahamane ya tabbatar da sace dan kasar Italyan yana mai cewa jami’an tsaron Nijar sun bazama neman ceto shi.

Yankin Tillabery da aka sace dan Italyan yankin ne da ke Makwabtaka da Mali da Burkina Faso kuma yanki ne da ke fuskantar hare haren yan ta’adda da ke gwagarmaya da makamai daga Mali 

A 'yan watannin da suka gabata ma wasu wadanda kawo yanzu ba a san ko su wanene ba sun sace wani dan kasar Jamus da ke aikin Jinkai a yanki Ayerou da ke makwabtaka da Mali duk dai a kasar Nijar