An nemi Musulmin Najeriya su hada kansu | Labarai | DW | 29.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nemi Musulmin Najeriya su hada kansu

Sarkin Musulmin Najeriya ya ce hadin kai tsakanin Musulmin kasar zai taimaka wajen warware ire-iren matsalolin da ke addabarsu a yanzu haka.

default

Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Sa'ad Abubakar na Uku

Sarkin Musulman ya furta hakan ne a wajen wani taron bita na kwanaki uku da aka shiryawa limaman masallatan Juma'a na jihohin arewacin Najeriyar 19 a birnin Minna na jihar Niger.

Wakilinmu da ke Minna Babangida Jibril ya ce Alhaji Sa'ad Abubakar wanda ya samu wakilcin guda daga cikin sarakunan arewacin kasar Alhaji Idris Musa ya ce dole ne al'ummar musulmi su maida hankalinsu wajen hada kawunansu don gudu tare a kuma tsira tare.

Wannan kira da taron limaman da sarkin na Musulmin Najeriya ya kira dai na zuwa ne bayan da lamura na tsaroa Najeriya musamman ma dai arewaci ke cigaba da tabarbare.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe