An musanta shirin Iran na janye kudadenta daga bankunan yamma | Labarai | DW | 21.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An musanta shirin Iran na janye kudadenta daga bankunan yamma

Mukaddashin gwamnan babban bankin Iran Mohammad Jafar Mojarad ya musanta sanarwar da kasar sa ta bayar cewa zata fara janye kudaden ajiyarta daga bankunan Turai zuwa na kasashen kudu maso gabashin Asiya. Mojarad ya fadawa kamfanin dillancin labarun kasar IRNA cewa babban bankin bai tanadi wani tsari na janye makudan kudaden ba. A ranar laraba da ta wuce gwamnan bankin ya ce Iran na shirin janye kadarorinta daga bankunan kasashen yamma don kare su daga wani takunkumi da MDD ka iya kakabawa kasar a dangane da shirin ta na nukiliya. A kuma halin da ake ciki shugaba Mahmud Ahmedi-Nijad yayi kira ga kasashen musulmi da su sake yin tunani game da huldar tattalin arziki tsakaninsu da kasashen yamma. Masu nazarin al´amuran yau da kullum sun kiyasce cewar Iran na da ajiyar kudi kimanin Euro miliyan dubu 41 a bankunan Turai.