An mikawa Ukraine fursunonin yaki 1,200 | Labarai | DW | 08.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An mikawa Ukraine fursunonin yaki 1,200

Shugaban Ukraine ya ce 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha sun mika fursunonin yaki dubu da dari biyu ga hukumomin kasar bayan cimma yarjejeniya tsagaita wuta.

Poroschenko in Mariupol 08.09.2014

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko

Petro Poroshenko ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi lokacin da ya kai wata ziyara birnin nan na Mariupol da ke gabashin kasar, ziyarar da shugaban ya kira ta ta karfafawa al'ummar birnin su kimanin dubu dari biyar gwiwa sanadiyyar irin barazanar da suka fuskanta a baya.

A jawabin nasa har wa yau shugaban ya ce ya umarci Ukraine din da su yi dukannin yadda za su iya don kare birnin da ma kasar baki dayanta daga barazara ta 'yan aware duk da cewar gwamnatin kasar da 'yan awaren sun cimma yarjejeniya tsagaita wuta a makon jiya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal