An kori shugaban ma′aikatar Shige da Ficen Najeriya | Labarai | DW | 22.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kori shugaban ma'aikatar Shige da Ficen Najeriya

Wata Sanarwar Ofishin ministan cikin gidan Tarayyar Najeriya ta sanar da korar shugaban ma'aikatar Shige da Fice kasar na Immigration, tare da manyan membobnin ofishinsa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori shugaban ma'aikatar Shige da Ficen kasar da ma manyan membobin ofishinsa a ranar Jumma'a (21.08.2015), wanda ofishinsa ke karkashin wani bincike, bayan gano wani batun a visa da aka samarwa wani mai Shehin Malami mai tsatsauran ra'ayi wanda shekaru biyu ana neman sa ruwa a jallo sakamakon rawar da ya taka a wani fada mai muni da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin kasar Lebanon 18 a shekarar 2013.

Sanarwar ofishin ministan cikin gidan kasar ta Najeriya dai ta ce an kori shugaban ma'aikatar Shige da Ficen ne ta immigration David Shikfu Parradang kai tsaye, sai dai sanarwa bata bayyana wasu dalillai na yin hakan ba, amma kuma ana ganin hakan na da nasaba da raunin da ake ganin wannan ma'aikata tana da shi wajan bincikar masu shige da ficin kasar ta Najeriya musamman ma a wannan lokaci da ake fama da matsalar tsaro.