1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kori rasha daga majalisar Turai

Abdoulaye Mamane Amadou
March 16, 2022

Majalisar Tarayyar Turai ta kori Rasha daga cikin mambobinta a hukumance a wani mataki na nuna adawa da mamayar da kasar ke yi wa Ukraine.

https://p.dw.com/p/48afC
Frankreich Russland Ukraine EU Krieg Flaggen
Hoto: Jean-Francois Badias/AP/picture alliance

Tun a ranar Talata majalisar ta kada kuri'ar fitar da Rasha daga cikinta kafin daga bisani a wannan Laraba kwamitin amintattu na majalisar ya amince da matakin a yayin wani taron gagagwa da ya gudanar.

Rasha da ta kasance mamba a majalisar Turai tun a shekarara 1996, sai dai ta sanar da ficewa cikin majalisar bayan da ta zargi kasashen da yi mata barazana.

Manazarta dai na ganin matakin fitar da Rashar daga majalisar ka iya jefa 'yan kasar cikin wani garari na rashin samun cikakkiyar kariya daga kotun kare hakin bil'Adama ta Turai.

Wannan ne karo na biyu a tarhin Turai da wata kasa ke ficewa daga majalisar, tun bayan makamancinsa da Girka ta yi a shekarar 1969, kafin ta sake dawowa a shekarar 1974.