1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kori jami'an diflomasiyar Rasha 100

Yusuf Bala Nayaya
March 26, 2018

Firaminisatar Birtaniya Theresa May ta bayyana cewa kasashe18 sun nuna goyon baya cewa za su sallami jami'an leken asiri sama da100 a matsayin martani ga Rasha bayan zarginta da kisan tsohon jami'in leken asirinta.

https://p.dw.com/p/2v1mh
Großbritannien Theresa May, Premierministerin
Hoto: Reuters/Parliament TV

Kasashen Amirka da Kanada da Ukraine da kasashe 15 daga Kungiyar Tarayyar Turai sun bi sahu wajen tisa keyar jami'an diflomasiyar Rasha bisa zarginsu da zama jami'an leken asiri da ke aiki kamar jami'an diflomasiya.

Firamanistar ta Birtaniya May ta fada wa majalisar dakoki a Birtaniya cewa wannan shi ne kora mafi girman da jami'an na Rasha suka taba ganin babbar kora a tarihi:

"Na samu hadin kai daga abokanmu da kawaye daga EU da Amirka ta Arewa da mambobi na NATO da sauransu." A cewar May dai halayyar da Rasha ke nunawa babbar barazana ce ga kafatanin kasashen yammacin duniya.