1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe 'yan IS a Masar

April 11, 2017

'Yan sandan kasar Masar sun kashe wasu da ake zargin mayakan kungiyar IS ne su bakwai a kudancin birnin Assiut. An dai zargi mayakan ne da kokarin kai hare-hare kan wasu majami'u na kasar.

https://p.dw.com/p/2b1fq
Ägypten Polizei auf dem Tahrir Platz in Kairo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Nabil

Ministan cikin gidan kasar ta Masar, ya ce da farko dai yan bindigar IS din sun budawa 'yan sanda wuta su kuma 'yan sandan suka mayar da martani. An zargi mayakan na IS da kokarin kai harin ta'addanci kan wasu majami'u da gidajen mabiya addinin Kirista da wasu muhimman cibiyoyin tsaro da ma na tattalin arziki.

Wannan artabun na zuwa ne kwana guda da kaddamar da wasu hare-haren bama-bamai kan majami'u biyu a biranen kasar biyu, da suka snadiyyar  mutuwar akalla mabiya 46. Kazalika akwai wasu sama da mutum 100 da suka jikkata a hare-haren ranar Lahadin da ta gabata.