An kashe sojojin Faransa biyu a Afghanistan | Labarai | DW | 26.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe sojojin Faransa biyu a Afghanistan

An kashe sojojin Faransa biyu na wata runduna ta musamman a wata musayar wuta da mayakan Taliban a gabashin Afghanistan. Wata sanarwa da ma´aikatar tsaron Faransa a birnin Paris ta bayar ta nunar da cewa wasu sojojinta biyu sun samu raunuka. Faransa dai na da sojoji kimanin 200 dake aiki da kawancen sojojin da Amirka ke wa jagoranci a yakin da ake yi da ´yan ta´adda musamman a yankin Spin Boldak dake kusa da kan iyaka da Pakistan. Wasu sojojin ta 800 kuma na aiki karkashin lemar rundunar ISAF dake karkashin jagorancin kungiyar tsaro ta NATO.