An kashe shugaban Taliban na Pakistan | Labarai | DW | 01.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe shugaban Taliban na Pakistan

Hukumomin Pakistan sun ce wani jirgin yakin Amurka marar matuki ya hallaka madugun kungiyar da ke gwagwarmaya da makamai

Pakistani Taliban chief Hakimullah Mehsud (C) sits with other militants in South Waziristan, in this file still image taken from video shot October 4, 2009 and released October 5, 2009. A U.S. drone strike in Pakistan killed Hakimullah Mehsud, the head of the Pakistani Taliban, on November 1, 2013, security sources told Reuters, the latest in a series of blows to Pakistan's most feared militant group. REUTERS/Reuters TV/Files (PAKISTAN - Tags: CIVIL UNREST OBITUARY)

Shugaban Taliban a Pakistan Hakimullah Mehsud wanda jirgin yakin Amurka ya hallaka

Wani jami'in tsaron Pakistan din da ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ce shugaban na Taliban Hakimullah Mehsud ya gamu da ajalinsa sakamakon harin da jirgin yakin na Amurka ya kai, a inda ya ke a arewacin Waziristan.

A da dai an sha bayyana cewar an hallaka Mehsud, sai kuma daga baya ya bayyana. To amma a wannan karon jami'an na tsoron Pakistan, sun ce tabbas madugun na 'yan Taliban din ya riga mu gidan gaskiya.

Ita ma dai kungiyar Taliban a Pakistan, ta tabbatar da mutuwar jagoran na ta, har ma ta bayyana cewar za a yi masa jana'iza a gobe Asabar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita:Usman Shehu Usman