An Kashe mayakan IS a Masar | Labarai | DW | 09.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An Kashe mayakan IS a Masar

'Yan sanda a Masar, sun kashe wasu da ake ganin 'yan bindigan IS ne su 14, a wani farmaki da suka kai har tungarsu 'yan jihadin a gabashin lardin Islamiyya.

Mahukunta a Masar, sun ce sun halaka 'yan bindigan IS din ne su 14, a farmaki da suka kai har maboyar 'yan jihadin a gabashin lardin Islamiyya. Sanarwar masu kayan sarkin na zuwa ne kasa da sa'o'i 48 da IS ta kaddamar wani hari a kan sojin kasar.

A cewar ministan harkokin cikin gidan kasar ta Masar, 'yan sandan sun afka wa mayakan na IS ne a gabashin lardin Islamiyya yankin da IS din ke da sansani a can. Gwamnatin Masar ta kuma ce biyar daga cikin 'yan bindigan, na cikin jerin wadanda da ma take nema 'ruwa a jallo'.

Ko a Juma'ar da ta gabata ma dai mayakan na tarzoma sun kaddamar da hare-hare a wasu shingayen bincike da ke yankin Sinai, inda suka yi ruwan Bama-Bamai gami da albrusai, sai dai jami'ai sun yi ikirarin kashe su da dama.