An kammala taron yanayi a birnin Bonn | Labarai | DW | 04.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala taron yanayi a birnin Bonn

Mahalarta taron sun tabka mahawara dangane da yarjejeniyoyin shawo kan sauyin yanayi

default

Norbert Röttgen

An kammala taro kan yanayi a birnin Bonn tare da  cimma wasu matakai dangane da shawo kan matsalar ɗumamar yanayi. Sai dai kusan babu nasarar da aka samu danagane da sabuwar yarjejeniyar ƙasa da ƙasa. Ƙasashe 40 suka halarci taronda da ƙasashen Jamus da Mexico suka ɗauki nauyin gudanarwa, gabannin taron da zai gudana a Nuwamba a birnin Cancun. Jami'ai sun shaidar dacewar, mahawara a wurin taron ya bada haske, kana ministan harkokin makamashi na Jamus Norbert Roettgen yayi alkawarin bayar da Euro miliyan 350 domin kare gadun jeji, kana Euro miliyan 850 domin inganta fasaha a  ƙasashe masu tasowa.

Mawallafiya: Zainab mohammed Edita: Ahmad Tijani Lawal