An kammala kada kuri´a a zaben shugaban kasar Liberia | Labarai | DW | 08.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kammala kada kuri´a a zaben shugaban kasar Liberia

Shekaru biyu bayan kawo karshen yakin basasan Liberia na tsawon shekaru 14, a yau talata al´umar kasar sun jefa kuri´a a zaben shugaban kasar na farko. An dai yi takara ne tsakanin hanshakin mai arziki kuma tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa George Weah da Ellen Jonhson Sirleaf masaniyar harkokin tattalin arziki kuma tsohuwar jami´ar bankin duniya. Jami´an wanzar da zaman lafiya na MDD dake cikin wata tawaga ta mutum dubu 15 suka sa ido a zaben na yau talata, wanda hukumomi suka ce an yi shi cikin kwanciyar hankali da lumana. Ana fatan samun cikakken sakamakon zaben cikin makwanni biyu. A zagaye na farko na zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Oktoba babu wanda ya sami adadin kuri´un da ake bukata ta samun rinjaye.