An kame sojojin Najeriya kan zargin yi wa yaki da ta′adda makirci | Siyasa | DW | 24.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An kame sojojin Najeriya kan zargin yi wa yaki da ta'adda makirci

Wasu manyan da kuma kananan hafsoshi suka shuga hannu saboda zargin da ake musu na shirya yin zagon kasa ga yakin da Najeriya ke yi da Boko Haram.

Wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar wacce kakakinta Kanar Sani Usman Kuka Sheka rattaba wa hannu ta nemi kafafan yada labarai da su yi takatsatsan da irin wadannan masu zagon kasa wanda ta ce suna neman yin amfani da kafafan sadarwa na zamani don cimma manufarsu.

Manufar wadanda ake zargi da shirya zagon kasar kamar yadda sanarwar ta fayyace ita ce bata sunan rundunar sojoji da kuma kashe musu guiwa a ayyukan tabbatar da tsaro da ya addabi shiyyar Arewacin Najeriya.
Ana kuma zargin akwai wasu fararen hula da ke taimakawa wajen yi wa sojojin makarkashiya a kokarinsu na daklie ayyukan kungiyar Boko Haram a wa'adin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shata musu wato karshen wata mai kamawa. Ga karin bayanin da Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya yi ta wayar tarho kan wannan batu.

"Ana nan ana binciken wadannan sojojin. Sun so su yi amfani da kafafan yada labaru musamman na zamani. Muna dangantaka ta kut da kut da kafafan yada labarai, muna kira gare su da sauran jama'a da kar su saurari wadannan sojoji masu yin batancin, su kuma lura."

Nigeria Abuja Bombenanschlag

Bincike bayan harin bam a Najeriya

Sai dai sanarwar ba ta fayyace ko su waye ake binciken da ma yawansu da kuma masu hada baki da su a fararen hula ba. Dama dai ana zargin cewa koma baya da ake samu a yaki da Boko Haram na da nasaba da zagon kasa da wasu daga cikin sojojin ke yi.

Bata-gari a cikin rundunar sojoji

Masu fashin baki kan harkokin tsaro sun bayyana cewa matakin da sojojin suka dauka na binciken masu yi musu zagon kasa abu ne mai amfani don ta haka ne za a iya gane baragurbi a cikin sojojin.

Hamza Umar Usman daya daga cikin masu sharhi kan al'amuran tsaro ne a Najeriya wanda ya ce:

"Ko da yake na ba soji ba ne, amma bisa dokokin aikin babu yadda da kowa. Abokinka a yau na iya zama abokin gabarka gobe. Muna kira gare su da suka kara bude kunnensu da idanunsu da basirarsu a kame wadannan bata-gari a cikinsu. A gurfanar da su. Domin wannan cin amanar kasa ne."

Talakawan Najeriya kuma nema suka yi rundunar Sojojin ta fadada wannan bincike domin gano sauran masu yi makarkashiya a wannan yaki da Kungiyar Boko Haram. Comrade Garba Tela Herwa gana Gombe wani mai gwagwarmayar kare hakkin talakawa ne a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.

"Su fadada yawan binciken da suke yi kan masu yi musu zago kasa, saboda ka da su hana su cimma nasara a yakin da suke yi da 'yan ta'adda."

Rundunar Sojojin dai ta yi alkawarin sanar da al'umma abubuwan da ta gano a binciken da ta gudanar kan jami'an na ta da kuma masu taimaka musu.

Sauti da bidiyo akan labarin