1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama wata 'yar jarida a Jamhuriyar Nijar

June 11, 2020

Kungiyar Amnesty International ta bayyana cewar an kama wata 'yar jarida, Samira Sabou a Jamhuriyar Nijar bisa tuhumarta da rubutun batanci a shafinta na blog kan badakalar kudin makamai.

https://p.dw.com/p/3dcWT
Symbolbild Medien in Niger
Hoto: DW/Bilderbox.com

Wani da ga na kusa da Shugaba Mahamadou Issoufou ne ya shigar da karar Samira sabou, a cewar kafofin watsa labarai da dama na kasar ta Nijar. Cikin sanarwar da ta wallafa a shafukan sada zumunta na zamani, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce tsare 'yar jarida Samira Sabou ba wani abu ba ne illa kawo tarnaki ga ayyukan kungiyoyin fararen hula da kuma kafafen yada labarai don dakile badakalar makamai.

Mai shari’a ya ba da sanarwa a ranar 8 ga Afrilu cewa a bude bincike kan badakalar makamai da ta barke a watan Fabrairu, bayan da wani binciken da Shugaba Issoufou ya nemi a gudanar ya bayyana adadin kudaden da aka biya wajen sayen makamai a fafatawa da masu jihadi a kudu maso gabas da kuma yammacin kasar.