An kama jigon barayin mutane a Najeriya | Labarai | DW | 20.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama jigon barayin mutane a Najeriya

Rundunar jami'an 'yan sanda a Najeriya, ta ce ta kama wani zarton mai garkuwa da mutane da take nema ruwa-a-jallo, bayan zargin sojoji da kubutar da mutumin.

A ranar shida ga wannan watan ne 'yan sandan na Najeriya, suka zargi sojojin da kashe masu wasu jami'ai uku da suka kware wajen cafke masu garkuwa da mutane, lamarin da ya haddasa nuna wa juna yatsa tsakanin rundunonin biyu.

Cikin wata sanarwa kakabin 'yan sandan kasar, Frank Mba, ya tabbatar da kama Hamisu Bala Wadume, da ake nema afujajan.

Wani dan gajeren faifan bidiyo ta ya fito a shafin twitter mallakin 'yan sandan, ya nuno mutumin na tabbatar da ikirarin.

'Yan Najeriya da dama dai na zargin kasancewar hannun wasu bata-garin jami'an tsaron kasar, cikin harkar garkuwa da mutane da ake hada damman miliyoyi cikin dan kankanin lokaci.