An kakabawa Masood Azhar takunkumi | Labarai | DW | 02.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kakabawa Masood Azhar takunkumi

Hukumar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Masood Azhar jagoran kungiyar Jaish-i-Mohammed dake Pakistan takunkumi bayan da kungiyar ta sanar da daukan alhakin harin daya afku a yankin kashmir.

Masood Azhar (picture-alliance / dpa)

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Pakistan Mohammed Faisal ne ya tabbatar da hakan yayin wata ganawar gaggawa da ya yi da 'yan jarida a Islamabad babban birnin kasar, ya kuma kara da cewar yanzu haka kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da kudaden Azhar da kuma haramta masa yin tafiye-tafiye. Wannan mataki dai na zaman nasara a bangaren Indiya wacce ta jima tana rokon Majalisar Dinkin Duniya ta kawo mata agaji game da harin da ya kara tsamin dangantakar kasashen biyu kan yankin na Kashmir. Pakistan dai ta bayyana cewar har yanzu bincike bai tabbatar da cewar kungiyar da Azhar ke jagoranta ce ta kai wannan hari ba.