An kai wani sabon hari a jihar Borno | Labarai | DW | 03.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai wani sabon hari a jihar Borno

Mutane akalla 11 sun mutu sakamakon harin da ‘yan Kungiyar Boko haram suka kai a safiyar wannan Jumma'a a garin Miringa da ke karamar hukumar Biu ta jihar Borno.

Wadanda suka tsira da rayukansu cikin wannan hari, sun bayyana cewa 'yan bindigar sun shiga garin ne da babura, kuma sun bi gida-gida inda suka zabi mutane suka fita da su bayan gari sannan suka harbesu. Yawancin wadanda aka hallaka mutane ne da suka gudu daga garuruwan da 'yan Kungiyar suke iko da su wanda ake zaton sun ki shiga cikin mayakan Kungiyar ne.

Rahotanni da ke fitowa daga garin Malari a karamar hukumar Kwanduga ma na cewa wata 'yar kunar bakin wake ta hallaka mutane 12 bayan da ta kutsa kai cikin wani masallaci ta kuma tada bam da ke daure a jikinta yayin da suke sallar azahar a jiya Alhamis. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa kafin mutanen su shiga masallaci sai da suka kori matar, inda bayan sun tada sallah ta kutsa masallacin da gudu. Yanzu haka an kai gawakin mutane a asibitin Kwastam da ke Maiduguri.

A wata sanarwa da fadarsa ta fitar a wannan Jumma'a Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa a kasar wanda ya kirasu na rashin imani da 'yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa tun bayan rantsar da shi a karshen watan Mayu da ya gabata, wanda kawo yanzu ya yi sanadiyyar rasuwar mutane a kalla 145. Sanarwar ta fadar shugaban kasar ta ce wannan wani babban dalili ne na gaggauta samar da dakarun hadin gwiwar nan na tafkin Chadi da za su yaki 'yan kungiyar.