An kai harin bam a Chadi
August 14, 2019Talla
Rahotannin da ke fitowa daga N'Djamena babban birnin kasar Chadin na cewa wata 'yar kunar bakin wake ce ta kaddamar da harin da ya hallaka mutum shida ciki har da wani jami'in soja guda.
Lamarin wanda ya faru a gundumar Kaiga-Kindjiria, ya kuma jikkata wasu mutanen da dama a cewar wata majiyar da ta fi son a sakaye sunanta.
Babu dai wata kungiyar da ta dauki alhakin harin da aka kaddamar da safiyar wannan Laraba, sai dai ana danganta shi da aika-aikar mayakan Boko Haram.
Yankin Kaiga-Kindjiria dai, yanki ne na tafkin Chadi da ya hada kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadin.
Akalla hare-hare 10 ne mayakan tarzomar Boko Haram suka kaddamar a Chadi daga bara i zuwa halin da ake ciki.