An kafa dokara hana fitar dare a birnin Beirut | Labarai | DW | 26.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kafa dokara hana fitar dare a birnin Beirut

Rundunar sojin kasar Lebanon ta kafa dokar hana fitar dare a birnin Beirut bayan zanga zanga da daliban jamiar birnin suka yi a jiya ya bazu zuwa wasu sassa na birnin,inda akalla mutane 3 suka rasa rayukansu.

Rikicin wanda ya hada da harbe harben bindigogi tsakanin yan sunni da kuma shia ya mamaye batun gudumowar euro biliyan 6 da kasashen masu bada gudumowa suka gudanar jiya a Paris na kasar Faransa,tare da nufin sake gina kasar Lebanon bayan yakin Israila da Hezbollah.

Hankula sun fara tashi ne tun ranar talata lokacinda Hezbollah ta kira yajin aiki na gama gari domin tilasta gaggauta gudanar da zabe a kasar.