An harbo jiragen yakin Ukraine biyu | Labarai | DW | 23.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An harbo jiragen yakin Ukraine biyu

'Yan awaren Ukraine da ke goyon bayan Rasha sun harbo jiragen yakin sojin Ukraine guda biyu a yankin nan na Lugansk.

Mai magana da yawun rundunar sojin Ukraine din da ya tabbatar da wannan labarin ya ce jiragen sun fado ne a yankin da ke da tazarar kilomita 25 da inda jirgin nan na Malesiya ya fado a makon jiya.

Rundunar sojin Ukraine ta ce matuka jirgin sun yi kokarin kaucewa harin da aka kai musu da makamai masu linzami sai dai hakarsu ba ta kai ga cimma ruwa ba.

Ya zuwa yanzu dai ba a tantance halin da matuka jirgin ke ciki ba sai dai wata majiya ta da ba tabbatar da sahihancinta ba ta ce sun fice ba tare da samun raunuka ba.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar