An hallaka ′yan IS 500 a wata guda | Labarai | DW | 23.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka 'yan IS 500 a wata guda

Rahotanni daga Kobani inda ake dauki ba dadi da dakarun kawancen da Amirka ke jagoranta da kungiyar nan ta IS na cewar an hallaka 'yan IS din kimanin 500 cikin wata guda.

Kamfanin dillancin labarai na AFP da ya bada wannan labarin ya ce galibin wanda suka rasu din sun gamu da ajalinsu sanadiyyar hare-haren da ake kaiwa ta sama da kuma irin farmakin da dakarun Kurdawa ke kai musu.

Baya ga wanda suka rasu, wasu mayakan da dama sun jikkata kazalika rahotanni na cewar fararen hula da yawa ma sun rasu a wannan yukuri da ake na karya kashin bayan 'yan IS din.

Wannan dai na zuwa ne bayan da a Larabar da ta gabata Turkiyya ta amincewa dakarun Kurdawa daga Iraki su dari biyu da su shiga ta cikin Turkiyyan don isa yankin Kobani don fuskantar 'yan kungiyar ta IS.