An hallaka mutane da dama a Maiduguri | Labarai | DW | 02.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hallaka mutane da dama a Maiduguri

Akalla mutane 35 aka tabbatar sun mutu a wasu tawayan hare-hare da aka kai a birnin Maiduguri hedkwatar jihar Borno da ke arewa maso gabacin Najeriya.

Wasu tagwayen hare-hare da ake danganta su da na 'yan kungiyar Boko Haram da aka kai a wata unguwa ta birnin Maiduguri, sun yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 35 a cewar daraktan 'yan sandar jihar Lawan Tanko yayin da yake bayani a wannan Lahadin.

Sai dai a cewar wasu da suka gane wa idanunsu tarwatsewar bama-baman guda biyu a kusan lokaci guda, a yammacin ranar Asabar, yawan wadanda suka rasa rayukansu zai kai akalla mutane 50 sannan da dama sun samu raunuka, kana an kone shaguna da sauran wuraren sana'ar jama'a.

Tagwayen hare-haren sun wakana ne kusan a lokaci daya a unguwar dake da yawan al'umma ta Gomari da ke birnin na Maidugurin a jihar Borno inda ake ganin nan ne cibiyar kungiyar ta Boko Haram bayan kafuwarta a shekarar 2009 a garin Damaturu na jihar Yobe.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal