An fidda faifan bidiyon ′yan matan Chibok | Labarai | DW | 14.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fidda faifan bidiyon 'yan matan Chibok

An samu wani labari daga CNN da ke bada fatar cewa ta yiwu 'yan matan Chibok da aka sace shekaru biyu da suka gabata a Najeriya suna raye.

Wani faifan bidiyon da tashar talabijin din CNN ta watsa a jiya jajibirin cikar shekaru biyu da sace 'yan matan, ya nuna 15 daga cikin 'yan matan kimanin 300 da aka sace arewacin Najeriya. Faifan da aka yi imanin an dauke shi ne a watan Disamban bara, a ciki an nuna 'yan matan sanye da hijabi, kuma bisa ga dukkan alamu kungiyar Boko Haram da kanta ne ta mikashi ga iyalan 'yan matan. A shekaru biyu da suka gabata ne dai wani harin da kungiyar Boko Haram ta kai ta sace 'yan matan a makarantar kwanansu. Ammma ko da yake daga bisani wasu cikin 'yan mantan sun samu tserewa, sai dai har yanzu akasari suna hannun kungiyar.