An fadada taron tattaunawa kan Siriya | Labarai | DW | 29.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fadada taron tattaunawa kan Siriya

Shugabannin difalmasiyyar kasashen Amirka, Rasha, Turkiya da Saudiya, za su soma zagaye na biyu na taro kan kasar Siriya kafin daga bisani kasar Iran ta shiga tattaunawar.

A karon farko dai kasar Iran da ake wa kallon mai dasawa da shugaban kasar Siriya Bashar Al-Assad, za ta shiga cikin tattaunawar neman zaman lafiya kan rikicin kasar ta Siriya da zai gudana a birnin Vienna. Kakakin Ofishin diflomasiyyar kasar ta Iran Marzieh Afkham ya ce kasarsa ta yi nazarin wannan gayyata, kuma ta tsaida cewa shugaban diflomasiyyar kasar Mohammad Javad Zarif ne zai halarci taron tattaunawar.

Wannan dai shine karo na farko da Iran za ta halarci zaman taron kasa da kasa kan rikicin Siriya, inda a shekara ta 2012 bata halarci taron birnin Geneva na daya ba da ya gudana kan kasar ta Siriya, sannan kuma aka hana mata shiga tattaunawa ta biyu a shekara ta 2014 a taron na biyu na Geneva. Tun dai farkon rikicin kasar ta Siriya Rasha ta sha nanata cewar ya dace kasar Iran ta shiga tattaunawar.