An dakatar da tattara sakamako a Jihar Rivers | Labarai | DW | 10.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dakatar da tattara sakamako a Jihar Rivers

Rahotannin da ke zuwa mana daga Jihar Rivers na cewar yanzu haka an dakatar da bayyana sakamakon zaben saboda yamutsin da ya taso abin da ya sa jami'an hukumar zaben ke jin tsoro kan kare lafiyarsu.

Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Prof. Mahmoud Yakubu

Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Prof. Mahmoud Yakubu

Hukumar zabe ta kasa a jihar Rivers ta bayyana cewar ta dakatar da aikin karbar sakamakon zaben da ta fara tun jiya wanda zai kai ga bayyana wanda ya lashe zaben ''gwamna'' na Jihar,Hakan ta ce matakin  na da nasaba da dalilai da suka hada da barazana da rayuwarsu ta shiga a yanzu din.