1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shiga mataki na biyu na gasar cin kofin Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe SB
January 24, 2022

Ta ware wa Najeriya da Gabon a gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka, yayin da kamaru ke wanke kanta daga zargin fitar da sakamakon corona na jabu domin hana comores rawar gaban hantsi.

https://p.dw.com/p/460B9
Wasannin AFCON: Najeriya da Tunisiya
'Yan wasan Tunisiya da NajeriyaHoto: BackpagePix/Sports Inc/empics/picture alliance

A ci gaba da gudanar da gasar neman lashe cin kofin kwallon kafar kasashen Afrika a Kamaru, wasannin mataki na biyu sun fara gudana inda sakamakon suka sha bamban da hasashen da aka yi, inda Burkina Faso ta haye mataki na gaba.

Sabanin yadda aka zata tun da farko dai, Burkina Faso ta fatattaki Gabon daga AFCON duk da jan kati da aka bai wa dan wasanta Sidney Obissa bayan minti 67 da fara wasa. A minti na 28 da fara wasa ne Bertrand Traoré na Burkina Faso ya fara zura kwallo. Amma daga bisani dara ta ci gida bayan da Adama Guira ya ci da kansa ana dab da busan karshe. Sannan alkalin wasa ya soke kwallon da Abdoul Tapsoba ya zira bayan karin lokaci saboda satar gida da ya yi. A karshe dai bugun daga kai sai mai tsaron gida 7 da Burkina Faso ta ci ya tabbatar mata da tikitin zuwa zagaye na gaba, yayin da Gabon da aka yi waje da ita, bayan ta ci kwallaye shida.

Wasannin AFCON: Najeriya da Tunisiya
'Yan wasan TunisiyaHoto: BackpagePix/Sports Inc/empics/picture alliance

Ita Burkina Faso za ta yi wasanta na gaba da Tunisia, wacce ta ba da mamaki ta hanyar korar Najeriya daga AFCON.

Sannin kowa ne cewa Najeriya ce kasa daya tilo da ta samu nasara a daukacin wasanni uku da ta buda a matakin rukuni. Saboda haka aka yi hasashen cewa Super Eagles za ta kace-kaca da Tunisia a filin wasa na Rumde Adjia da ke Garoua. Sai dai babu wani abun da ya gudana kamar yadda aka yi wa Najeriya fata, musamman ma bayan dawowa hutun rabin lokaci, inda  Youssef Msakni na Tunisiya ya buga kwallo a raga. Hakazalika mintuna goma bayan cinsu kwallo, 'yan wasan Najeriya suka sake samun wani komabaya sakamakon korar Alex Iwobi daga filin kwallon lokaci kalilin bayan shigowarsa. Tun wannan lokaci ne Super Eagles ta kasa tabuka wani abin a zo a gani a gaban 'yan Tunisia.

Duk da bukatar sauye-sauye a tsarin wasan Super eagles da kocinta na riko ya bayyana, amma wasu 'yan najeriya sun tahallaka rashin nasarar a kan sakacinsa da kuma 'yan wasa na gaba

A wannan Litinin ne Guinea Conakry za ta kara da Gambia, yayin da Kamaru mai masaukin baki za ta yi da wasan da 'yar autan AFCON wato Comoros. sai dai kasar ta shiga hali na tsaka mai wuya sakamakon 12 daga cikin 'yan tawagarta suka kamu da covid-19 ciki har da koci Amir Abdou, da kuma uwa uba masu tsaron gida biyu. Wannan yana nufin cewa Comoros za ta yi wasa ba tare da kwararren mai tsaron gida ba. Amma dai wasu na zargin kamaru da amfani da matakin kiwon lafiya wajen musguna wa abokan hamayyarsu, saboda har yanzu ba dan wasan kamau ko daya da ya kamu da cutar.

A Jamus, laya ta yi wa manyan kungiyoyi kyaun rufi a mako na 20 na Bundesliga a musamman ma  Bayern Munich.

Wasan Bundesliga | Hertha da Bayern München
BundesligaHoto: Hannibal Hanschke/REUTERS

Yaya-Babba Bayern Munich ta bi Hertha Berlin har gida wajen doke ta da ci kwallaye 4-1 da suka samu daga 'yan wasa hudu daban-daban. Saboda haka Bayern Munich na ci gaba da zama a saman teburin Bundesliga da maki 49 tare da samar da tazarar maki shida tsakaninta da Yaya-Karama Borussia Dortmund mai maki 43. Hasali ma BVB wacce ta samu nasara ci 3-2 a kan Hoffenheim. Ita kuwa Leverkusen ta karfafa matsayinta na uku bayan da a gida BayArena ta yi wa Augsburg cin kaca 5-1. Godiya ta tabbata ga Moussa Diaby dan kasar Faransa da ya zura uku daga cikin kwallayen a raga.

Amma duk da wannan nasara, Leverkusen da ke da maki 35 a yanzu na da ratar maki daya ce kacal ta Union Berlin wacce ta lallasa Borussia Mönchengladbach da ci 2-1. A yanzu dai Freiburg ce ke a matsayi na biyar bayan da gasa wa VfB Stuttgart aya a hannu da 2-0.  A nata bangaren kuwa RB Leipzig ta samu nasararta ta uku a jere bayan da ta yi wasa bil hakki da gaskiya kuma ta doke VfL Wolfsburg ta koci Domenico Tedesco da  ci 2-0.

Wasan Bundesliga | Greuther Fürth da Mainz 05
BundesligaHoto: Wolfgang Zink/Sportfoto Zink/imago images

A sauran sakamakon, Greuther Fürth da ke zama kurar baya ta yi abin kai wai fitsari da kunfa inda ta samu nasararta ta biyu tun bayan fara kaka bayan da ta doke Mainz 2-1. Ita kuwa FC Cologne da ke matsayi tsaka-tsakiya ta tashi ne da ci 2-2 a wasan da ta yi da Bochum. Sai dai Armenia Bielefeld da ita ma ke jerin 'yan baya ga dangi ta samu nasara a kan Eintracht Frankfurt da ci 2-0.

Dan Kamaru Francis Ngannou wanda ya ci gaba da rike kambunsa na ajin masu nauyi na duniya na damben MMA bayan da ya doke Cyril Gane na Faransa a birnin Los Angeles na Faransa. Hasali ma a wani halin na ba sabonba, Shugaba paul Biya da kansa ya wallafa sakon taya murna ga dan damben, bayan da dimbin 'yan kamaru da suka hana idanunsu barci wajen kammlon damben a talabijin.