1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto daliban jinya 20 a Benue

Abdul-raheem Hassan
August 24, 2024

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da ceto daliban aikin jinya da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Benue, 'yan sanda sun ce ba a biya kudin fansa ba.

https://p.dw.com/p/4jt1q
'Yan sandan Najeriya
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture-alliance

Wasu kafofin cikin gida a Najeriya sun ruwaito cewa, gwamnati ta yi amfani da wasu jiragen yaki masu saukar ungulu wajen kubutar da daliban, tare da ikirarin kama wasu daga cikin 'yan bindigar.

Masu garkuwan sun dauke daliban na jami'ar Maiduguri da jami'ar Jos tare da likitoci, 'yan bindigar sun kuma nemi a biya su kudin fansa har naira miliyan 50. Najeriya ta jima tana fama da rikicin 'yan bindiga na masu satar mutane don neman kudin fansa.

Wata cibiyar tattara bayanan sirri a Najeriyar, ta kiyasata mutane 4,777 ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da su tun hawan shugaban kasar Bola AHmad Tinubu a watan Mayu na shekarar 2023 zuwa watan Agusta na shekarar 2024.