1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude gidauniyar tallafa wa Yemen

Mahmud Yaya Azare GAT
June 3, 2020

Kasar Saudiyya a bisa hadin gwiwar MDD ta bude taron kafa gidauniyar neman tallafin kudin sake gina kasar Yemen wacce yaki da kuma cututtuka suka daidaita. Taron na samun halartar kasashe 66 da kungiyoyi sama da 125.

https://p.dw.com/p/3dClI
Luftangriff im Jemen
Hoto: Reuters/Mohamed al-Sayaghi

Tare da hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya, kasar Saudiyya ta shirya taron gidauniyar tara tallafin kudaden agaji ga kasar Yemen, a daidai lokacin da talauci da cututtuka ke kara galabaita kasar wacce dama yaki ya gama daidaita ta.

Kimanin kasashe 66 da kungiyoyi na kasa da kasa 126 ne dai ke halartar taron kafa gidauniyar kudaden a kasar ta Yemen, wanda shi ne irinsa na biyu bayan wanda aka shirya a Geneva a shekarar 2017. Taron da aka gudanar da shi ta hanyar amfani da na,urar tattaunawa ta bidiyo daga nesa,wato Video conference, ya kudiri aniyar tara Dalar AmIrka biliyan biyu da rabi ne don tunkarar tarin matrsaloli da kasar ta Yemen ke fuskanta, inji Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres:

"A yau kasar Yemen ta tsunduma cikin babban bala,in da ba ya misaltuwa. Rashin cika alkawuran da aka yi ta yi a baya na tara mata tallafi, da yakin da ake ci gaba da gwabzawa, gami da bullar cutattuka, musamma annobar Corona, sun sanya rayuwar miliyoyin 'yan kasar cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai. Dama daga cikin yara kananan da yunwa da cutattuka suka yi wa illa, ko da sun rayu, za su ci gaba da zama na tsawon rayuwarsu cikin nakasa."

Luftangriff im Jemen
Hoto: Reuters/Mohamed al-Sayaghi

Mukaddashin shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, a kasar ta Yemen, Ayman Gharaibeh, ya ce tun kusan watanni shidan da suka gabata ayyukansu a kasar ta Yemen suka gama durkushewa saboda karancin kudi:

"Tabbas idan har babu kayan aiki, babu abun da za mu iya tabukawa a Yemen. Akwai kimanin mutane milyan tara da suka dogara kacokam kan agajin da muke gabatar musu, sakamakon raba su da mahallinsu da yaki ya yi. Ci gaba da zamansu cikin wannan mawuyacin yanayin ba karamar barazana ba ce ga tsaron kasar da ma a yankin baki daya."

Kasar Saudiyya da ke shirya taron, wacce kuma wasu 'yan kasar ta Yemen ke zargi da zama kanwa uwar gami ga halin ni 'yasun da  suka tsinci kansu ciki, sakamakon hare-haren da take ta ikirarin tana kaiwa don fatattakar 'yan Huthi, kasar ta Saudiya ta yi alkawarin bayar da gudummawar Dalar Amirka miliyan 525 inji walilinta a taron, Abdallah bin Abdul Azeez Alrubai'ah, mai bai wa Sarki Salman shawara kan lamuran ketare:

Jemen Tais Kämpfe mit Huthi Miliz
Hoto: Reuters/N. Quaiti

"A ko da yaushe,masarautar Saudiyya takan amsa kiran da Majalisar Dinkin Duniya ke yi na kawo wa kasar Yemen dauki. Kuma za mu ci gaba da yin hakan don rage wa 'yan kasar radadin da suke sha, sakamakon ayyukan mayakan sa kai a kasar. A koyaushe, masarautar Saudiyya tana nanata cewa, babu ta yadda za a iya mangance matsalar Yemen sai ta hanyar cimma zaman lafiya."

Tuni dai 'yan kasar ta Yemen suke ta nuna kyakkyawan fatan gidauniyar za ta zama fada da cikawa, ba kamar yadda aka saba yi a yi taro a waste ba, su kuwa sai dai su ji a salansa. A yayin da su kuwa 'yan tawayen Huthi ke siffanta taron da wani yunkuri na rufa- rufa a barnar da Saudiyya da kawayenta sukai tafka a kasar ta Yemen.