An bude taron kan harkokin tsaro a birnin Munich | Labarai | DW | 04.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kan harkokin tsaro a birnin Munich

Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gargadi Iran da ta hanzarta yin watsi da shirin ta na nukiliya. A lokacin da take jawabin bude taron kan harkokin tsaro a birnin Munich dake kudancin Jamus, Merkel ta yi kira ga gwamnatin birnin Teheran da ta amince da shawarwarin da gamaiyar kasashen duniya ta bayar da nufin gano bakin zaren warware wannan rikici. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kuma yi tir da kalaman da shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad yayi na kyamar Isra´ila tare da nuna shakku ga aukuwar kisan kiyashin da aka yiwa yahudawa a nahiyar Turai. Merkel ta ce Jamus ba zata iya jurewa irin taurin kai da Iran ke nunawa. Sakataren tsaron Amirka Donald Rumsfeld da sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jaap de Hopp Schefer na daga cikin mahalarta taron na bana.