An binne madugun ′yan adawa na Rasha | Labarai | DW | 03.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An binne madugun 'yan adawa na Rasha

Dubban mutane sun halarci grimama magudun 'yan adawa na Rasha da aka kashe

Dubban mutane sun yi girmamawa ta karshe a madugun 'yan adawa na kasar Rasha Boris Nemtsov, wanda aka bindige ranar Jumma'a da ta gabata, a birnin Moscow. Masu zaman makoki sun ajiye furenni domin girmama Marigayi Nemtsov wanda ya yi fice wajen sukar gwamnatin Rasha lokacin da yake raye.

Akwai jiga-jigan 'yan adawa da suka halarci girmama Marigayi Boris Nemtsov da ke zama tsohon mataimakin firamnistan kasar ta Rasha. Gwamnati ta ce ana binciken gano makisan.