Ku kawo karshen Boko Haram cikin watanni uku- Buhari
August 13, 2015Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sababbin hafsoshin sojan kasa, sannan ya umurce su da su kawo karshen hare-haren Boko Haram cikin watanni uku. Kungiyar wadda ta yi mubaya'a da kungiyar IS ta shafe shekaru shida tana aikata ta'asa musamman a yankin Arewa masu Gabashin Najeriya, ta'asar da ta kai ga salwantar rayuka fiye da 15,000.
Buhari ya fada wa hafsoshin sojin a Abuja cewa dole su zage dantse, su hada karfi da sauran masu ruwa da tsaki don samar da wani gagarumin aiki da zai kai ga samun sakamakon da ake bukata na kawo karshen tarzomar cikin watanni uku.
Buhari wanda ya hau kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu ya gaggauta maye gurbin shugabannin rundunar sojan kasa da na sama da na ruwa da kuma shugaban dakarun tsaro a wani matakin sake dubarun yaki da Boko Haram.