1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amurka za ta tura dakarunta 200 Najeriya don horas da sojoji

February 11, 2026

Amurka da Najeriya sun cimma matsayar girke dakaru a Najeriya don horas da sojin kasar dabarun yaki da 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/58UDV
Sojojin Amurka
Sojojin AmurkaHoto: Brian Cassella/Chicago Tribune/TNS/ABACA/picture alliance

Mai magana da yawun hedikwatar rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran AFP cewa shirye-shirye sun kammala na tarbar sojojin Amurka a Najeriya, duk dai a kokarin murkushe 'yan ta'addan da ke ci gaba da kashe fararen hula musamman a shiyyar arewacin kasar. To sai dai Janar Uba ya ce sojojin Amurkan ba za su shiga fagen daga ba, kawai za su bada horo ne ga sojojin Najeriya kan yaki da ta'addanci.

Karin bayani:Amurka ta kai hari kan 'yan ta'adda a Najeriya

Jaridar Wall Street Journal ce ta fara wallafa labarin zuwan sojojin Amurka akalla 200 Najeriya. Abuja dai na fuskantar matsin lamba daga Washington tun bayan zargin da Donald Trump ya yi cewa na ana kashe Kiristoci a kasar, wanda hakan ya haifar da rudani da kuma martani daban-daban daga ciki da wajen Najeriya.