1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka ta jaddada adawa da kutsen Isra'ila a Rafah

April 8, 2024

Amurka ta jaddada adawarta ga matakin Isra'ila na kutsawa Rafah ta kasa, a daidai lokacin da Benjamin Netenyahu ya saka rana domin kai farki a birnin da Falasdinawa kusan miliyan guda da rabi ke tsugune.

https://p.dw.com/p/4eYnn
USA Israel Joe Biden Benjamin Netanjahu
Hoto: Miriam Alster/UPI Photo/imago images

A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a maraicen ranar Litinin ne kakakin fadar mulki ta White House Matthew Miller  ya nanata cewa Amurka ba ta goyon bayan shirin Isra'ila na afkawa Rafah ta kasa domin fatattakar mayakan Hamas, shirin da tun da farko Washington ta bayyana a matsayin mai matukar hadari.

Karin bayani: Gaza: Isra'ila ta dage kan afkawa Rafah

A daya gefe kuma jakadan Isra'ila da ke Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan bukatar Falasdiwa na amincewa da yankinsu a matsayin kasa mai cekekken 'yanci, a daidai lokacin da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya fara nazari a hukumance kan wannan bukata da ta fara samun karbuwa a wajen wasu manyan kasashe.

Karin bayani: Duniya na muradin kafa kasar Falasdinu

A lokacin da yake tsokaci a babban zauren majalisar, Gilad Erdan ya ce amincewa da wannan bukata babban kuskure ne da ka iya kara karfin barazanar 'yan ta'adda a yankin.

Kazalika mista Gilad Erdan ya kara da cewa yunkurin amincewa da Falasdinu a matsayin kasa mai cikekken 'yanci na iya ruguzasa duk wani kokari na sansanta yakin da ya sake kunno kai a yankin a ranar bakwai ga watan Oktoban bara. 

Gwamnatin Isra'ila dai na adawa da wannan shiri da ke samun goyon bayan wasu kasashen duniya ciki har da Amurka na samar da mafita ga rikicin yankin ta hanyar bai wa Falasdinawa cikkeken 'yancin da suka dade suna mafarkin samu.