1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta ce ta kai hare-hare 6000 a Iran

March 12, 2026

Rundunar sojin Amurka ta ce sojojin ta ce ta kai hare-hare kan wurare kusan 6,000 a Iran tun bayan fara rikicin, inda ta lalata jiragen ruwa na Iran kusan 90 da kuma na’urorin shimfida nakiyoyi sama da 30.

https://p.dw.com/p/5AJ6H
Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Samuel Corum/Sipa USA/picture alliance

Rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya, wato CENTCOM, ta ce dakarun Amurka  sun yi amfani da kayan yaki dabam-dabam da suka hada da jiragen yaki masu linzami, jiragen sama na yaki da kuma jiragen ruwan yaki wajen kai wadannan hare-hare.

Har ila yau, rundunar ta ce hare-haren sun fi karkata kan hedikwatar rundunar sojin Iran IRGC da cibiyoyin tattara bayanan sirrin Iran da kuma wuraren kerawa da ajiye makamai masu linzami.