Amurka da Isra'ila sun sake far wa Iran da Lebanon
March 8, 2026
Isra'ila da Amurka sun kai sabbin hare-hare a Lebanon da Tehran yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta a yau Lahadi.
Hare-haren na kudancin Lebanon, da babban birnin ƙasar Beirut da kuma ma'ajiyar man fetur a Tehran sun yi mummunan barna.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi alƙawarin cewa za a ga “abubuwan mamaki” a mataki na gaba na yaƙin.
Na rufe kofar tattaunawa da Iran - Trump
A nata ɓangaren, Iran ta kai hari kan wata tashar tace ruwa a Bahrain. Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce suma wani harin sama na Amurka ya lalata tashar tace ruwansu a Iran da ke Qeshm.
An jiyo shugaban Iran Massud Peseschkian na cewa kasarsa ba za ta mika wuya ga Amurka ba kuma neman afuwa da yayi wajen makwabtansa kasashen Larabawa ba mika wuya bane kamar yadda Trump ya yi ikirari.
Trump na son kasar Iran ta mika kai bori ya hau
Starmer ya tattauna da Trump
A daya bangaren, Firaministan Burtaniya, Keir Starmer, ya tattauna da shugaban Amurka, Donald Trump, kan haɗin gwiwar soji tsakanin ƙasashen biyu, bayan sukar da Trump ya yi kan matsayin Burtaniya a yaki da Iran.
Rahotanni sun ce matakin da Starmer ya ɗauka na ƙin ba da izini a yi amfani da sansanin Burtaniya wajen kai hare-haren soja ya jawo suka daga Trump.
Sai dai daga baya Starmer ya ba da izini ga Amurka ta yi amfani da wasu daga cikin sansanonin Burtaniya don matakan “kariya” kawai daga makamai masu linzami na Iran.
Bayan rahotannin cewa Burtaniya na shirin tura jirgin ruwan yaki mai ɗaukar jiragen sama zuwa Gabas ta Tsakiya, Trump ya wallafa a ranar Asabar cewa “a ƙarshe Birtaniya tana tunanin tura jiragen guda biyu, amma yanzu ba a buƙatar su.”
Wata kakakin gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa shugabannin biyu sun tattauna a yau Lahadi da rana kan yakin na Iran.
Isra'ila ta sha alwashin ganin bayan duk wani sabon shugaba da aka nada a Iran
An yi zanga-zangar kyamar yaki a Sfaniya
Dubban mutane a Sfaniya sun gudanar da zanga-zanga domin neman a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Iran.
An gudanar da jerin gwanon a sassa daban-daban na ƙasar a ranar Lahadi domin neman zaman lafiya albarkacin ranar mata ta duniya.
Mutane da dama sun riƙe alluna masu ɗauke da saƙon “A’a ga Yaƙi!”, yayin da suka riƙa maimaita kalaman da firaministan ƙasar, Pedro Sánchez, ya faɗa sau da dama a kwanakin baya.
A babban birnin ƙasar, Madrid, ‘yan sanda sun kiyasta cewa mutane 35,000 ne suka halarci zanga-zangar.
Yawancinsu mata ne, amma akwai maza kuma masu shirya zanga-zangar sun ce adadin mahalartanta ya kai mutane 180,000.