Amnesty ta zargi manyan sojin Najeriya da aikata laifin yaki | Labarai | DW | 03.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amnesty ta zargi manyan sojin Najeriya da aikata laifin yaki

A cikin rahoton da ta bayar kungiyar ta Amnesty International ta yi kira da a kaddamar da bincike kan wasu jam i'an sojin Najeriya su biyar.

Kungiyar Amnesty International ta ce akwai kwararan hujjoji ga kotun hukuntan manyan laifuka don kaddamar da bincike kan wasu jami'an sojin Najeriya bisa aikata laifin yaki a yakin da ake yi da Boko Haram. A cikin wani sabon rahoto da ya kunshi daruruwan hirarraki da ma wasu majiyoyin soji da kuma wasu bayanai da aka tsegunta daga ma'aikatar tsaro, kungiyar ta zargi manyan jami'an soji biyar da aikata laifin yaki. Amnesty na zargin dakarun tsaron Najeriya da 'yan civilian JTF da halaka dubban mutane da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba. Amnesty ta kuma yi zargin cin zarafin wadanda sojojin ke tsare da su. Amma sabon rahoton ya ce Amnesty ta yi imani sabbin shaidun da ke cikin rahoton wanda ta tura wa ICC kwafi, ya kai a sake bude wani binciken.