1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta zargi jami'an tsaron Najeriya da aikata laifukan yaki

March 31, 2014

Kungiyar Amnesty International ta zargi Sojojin Najeriya da mayakan Kungiyar Boko Haram, da kashe mutane 1,500 da wasu laifukan cin zafarin bil'adama.

https://p.dw.com/p/1BYnJ
Hoto: DW/Katrin Gänsler

Kungiyar mai fafutukar kare hakin bil'adama ta kasa-da kasa, cikin wani kira da tayi, ta ce a kalla mutane 1500 ne aka kashe a Arewa maso Gabashin Najeriya, wanda alhakin hakan ya rataya ne a wuyan sojojin kasar da 'yan kungiyar ta Boko Haram tun daga farkon shekara kawo yanzu, tare kuma da yin kira ga kasashen duniya da su aiwatar da bincike kan abubuwan da suka wakana a wannan kasa.

Sai dai ita ma daga nata bangare hukumar agajin gaggawa ta Tarayyar Najeriya NEMA, da ta fitar da nata rahoton ta tabbatar da cewa an kashe fiye da mutane 1000 yayin da wasu mutanen dubu 250 suka bar matsugunnan su.

Daga na ta bangare kungiyar kare hakin bil'adama ta Human Rights Watch, da ta fitar da nata rahoton a ranar 14 ga watan Maris, ta ce a kalla mutane 700 ne suka mutu daga farkon shekara zuwa wannan lokaci a Arewa maso Gabashin kasar.

Kungiyar ta Amnesty dai ta ce mafi yawan mutanen da aka kashe farar hula ne da ba su ji ba, kuma ba su gani ba, inda kuma ta nuna damuwar ta ga kashe wasu tarin mutane da suka gudu daga wani gidan kaso a ranar 14 ga watan Maris, inda ake zargin suna da alaka da kungiyar ta Boko Haram.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar