1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty International ta caccaki Najeriya

Yusuf BalaFebruary 1, 2016

Kungiyar ta bukaci a yi bincike kan wasu manyan sojoji tara a Najeriyar ciki kuwa har da manjo janar Ahmadu Muhammad ko da za a samu hannunsa cikin manyan laifuka.

https://p.dw.com/p/1Hmh5
Amnesty International Symbolbild
Alama ta kungiyar Amnesty InternationalHoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

A ranar Litinin din nan kungiyar Amnesty International ta yi sabuwar caccaka ga gwamnatin Najeriya wacce ta ce ta sake maida wani janar din soja kan mukaminsa bayan zarginsa da aikata laifin yaki.

Kungiyar da ke da sansani a a birnin London ta bukaci a bara da a gudanar da bincike kan wasu manyan sojojki tara a Najeriyar ciki kuwa har da manjo janar Ahmadu Muhammad ko da za a samu hannunsa cikin manyan laifuka da suka hadar da sanadi na rayukan sama da mutane 8,000 da aka rikesu tun a shekarar 2011.

A cewar kungiyar ta Amnesty Muhammad ya kasance shi ne kwamanda lokacin da sojoji suka far wa wasu mutane 640 da basa dauke da bindiga bayan wani farmaki da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a barikin Giwa da ke birnin Maiduguri jihar Borno Arewa maso Gabashin Najeriya.