Amirka za ta tura kwararrun sojoji Najeriya | Labarai | DW | 27.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta tura kwararrun sojoji Najeriya

Ma'aikatar tsaron Amirka na duba yiyuwar aikawa da sojoji ya zuwa Tarayyar Najeriya, domin baiwa sojojin kasar shawarwari kan yadda za a kawo karshen Boko Haram.


Idan Amirka ta aiwatar da wannan shawara, to hakan zai yi nuni da irin ci gaban da ake samu a huldar dipolomasiyya tsakaninta da Najeriya, inda a shekara ta 2014 dangantakar ta yi tsami tsakaninsu.

Gwamnatin da ta shude ta Goodluck Jonathan a baya ta nuna rashin jin dadinta ga matakin da kasar ta Amirka ta dauka na kin sayar wa Najeriyar makamai, bisa zarginta da take hakkokin bil-Adama musamman daga sojojinta, inda aka watse baram-baram bisa matakin horas da sojojin na Najeriya.

A watan Yuli dai da ya gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya samu kyaukkyawan tarbo daga hukumomin kasar ta Amirka.