Amirka za ta inganta tsaro a Afirka | Siyasa | DW | 26.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amirka za ta inganta tsaro a Afirka

Manufofin harkokin wajen Amirka kan sha'anin tsaro ka iya jefa muradun kasar a cikin kasada ganin yadda aikin rundunar sojan kasar a Afirka ya janyo cece-kuce bayan halaka wasu dakarun kasar a Nijar.

Mutuwar sojojin Amirka a Nijar ya sa kasar sake tunani kan hanyar tunkarar ayyukan ta'addanci da 'yan ta'adda, lamarin ya janyo jakadar kasar da ke Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley kai ziyara zuwa wasu kasashen Afirka da suka hada da Sudan ta Kudu gami da Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. Daya daga cikin muradun ziyarar shi ne kara matsin lamba kan shugabannin don samun zaman lafiya. Phil Clark ya kasance masanin harkokin siyasa na makarantar koyar da harkokin kasashen Afirka da Asiya da ke birnin London na Birtaniya.

"Mutuwar sojojin musamman na Amirka a Jamhuriyar Nijar ina tunani ya janyo gagarumar muhawara bisa aikin sojin Amirka a Afirka karkashin rundunar AFRICOM. Akwai Amirkawa da yawa wadanda suke mamakin kasancewar sojojin Amirka a wadannan kasashe na Afirka."

USA Florida Beisetzung Soldat David Johnson Witwe Myeshia Johnson

Matar daya daga cikin sojojin Amurka da ya rasa ransa a Nijar

Masana na ganin babban matsalar ita ce rashin fahimtar nahiyar Afirka daga bangaren shugaba Donald Trump na Amirka da jakadar kasar a Majalisar Dinkin Duniya  Nikki Haley, da kuma kwarewa bisa wannan fannin mai sarkakiya, haka lamarin ya ke tsakanin makusantan shugaban. Hady Amr manazarci kan manufofin Amirka ya nuna dari-dari kan wannan ziyara inda yake ganin hakan a matsayin hanyar tara bayanai kawai.

Galibi kasashen Afirka abin da suka bai wa fifiko shi ne samar da tsaro. Ita kanta jakadar kasar ta Amirka Nikki Haley ta bukaci ganin samun manufofin Amirka bisa nahiyar Afirka. Tun bayan kisan dakarun Amirka a Jamhuriyar Nijar lamarin aikin dakarun da ake kira AFRICOM ya sake dawowa bainar jama'a, inda Amirka suke neman amsoshi kan tambayoyin da suka shige musu duhu.

A cikin makonnin da suka gabata kalaman Donald Trump ya dauki hankalin mutane a nahiyar Afirka bayan ya zargi wasu abokansa da suke rige-rigen zuwa nahiyar domin samun arziki. Akwai masu tunanin cewa gwamnatin Trump za ta kirkiro wasu hanyoyin kasuwanci zai taimakawa 'yan kasuwar Amirka shiga nahiyar Afirka amma babu wanda yake da masaniya kan ribar da nahiyar ta Afirka za ta samu.