Amirka za ta horas da sojin Najeriya | Labarai | DW | 04.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta horas da sojin Najeriya

Shugaban tawagar 'yan majalisar dokokin Amirka da ke ziyara a Najeriya ya ce a shirye Amirka ta ke ta tallafawa dakarun Najeriya da horo don kawar da ta'addanci.

Dan majalisa Darrell Issa da ke jagorantar tawagar ya ce dakarun na Najeriya sun fi bukatar horo maimakon makamai wajen samun nasara a yakin da suke da 'yan ta'adda wanda suka yi sanadiyyar rasuwar dubban mutane a kasar da kuma kasashen da ke makotaka da ita.

Wadannan kalamai na Mr. Issa na zuwa ne bayan shi da 'yan tawagarsa sun yi wata ganawa da shugaba Muhammadu Buhari da manyan jami'an tsaron kasar kan halin da tsaro a Najeriya ke ciki.