1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta zargi Najeriya da take 'yancin addini

December 22, 2019

Amirka ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da za ta sanya wa idanu saboda zarginta da take hakkin gudanar da addini da mutum ke ra'ayi ba tare da wata tsangwama ba.

https://p.dw.com/p/3VDqj
Präsident USA Donald Trump
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Silbiger

Sakataren harkokin wajen Amirka Mr Mike Pompeo ya tabbatar da sanya sunan Najeriyar cikin wata sanarwar da ya sanya wa hannu.Hakan ya zo ne daidai lokacin da hukumar kula da kare 'yancin addini ta Amirkar, ta fitar da wani rahoton da ya bayyana Najeriyar daga cikin kasashen.

Wasu kasashen da matakin na Amirka ya shafa sun hada ne da kasar Iran da Pakistan da Rasha da Nikaraguwa da kuma kasar Kuba.Rahoton Amirka ya zargi Najeriya da take hakkin mabiya mazhabar Shi'a; da ma kasancewar wasu bangarorin kasar na bin tsarin Shari'ar addinin Islama.